Translate site
Wednesday, 2 September 2015
Google da Apple sun kulla dangantaka
Kamfanin Google ya mayar da manhajarsa ta Android wadda za
a iya daurawa ta yi aiki da ta Kamfanin Apple a manhajar
iOS.
Wannan ci gaba na nufin cewa masu agogon hannu na manhajar
Android za su iya amfani da wayar salula ta iphone a karo na
farko.
Hakan dai zai habaka kasuwar agogunan hannu na zamani kuma
zai zama kalubale ga kamfanin nan Apple.
Wannan sabon ci gaba na nufin masu agogon hannun za su iya
kiran waya ko su amsa kira.
Haka kuma za su iya duba sakonnin ka-ta-kwana na text, har ma
da duba lafiyar zuciyarsu ta hanyar yadda ta ke bugawa.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment