Translate site

Sunday, 13 September 2015

Alhazan Najeriya Basu cikin Wadanda Hatsari Ya Rutsa Dasu.


Amma alhamdulillahi zamu ce wannan abu bai shafe su ba ta bangare rasuwa ba sai dai an samudan kalilan na mutum ukku zuwa hudu da suka samu raunuka wadanda kuma raunukan ba wadanda suke barazana bane ga ainihi rayuwar su. Mutanen da kace sun samu raunukan an basu gado ne ko kuwa sun tafi sun ci gaba da harkokin su? ‘’A’a kamar yadda nayi bayani ai ba wani abu bane, irin dai dan buguwa ne haka, abubuwa ne ba masu tada hankali ba, wasun ma an basu magani an sallame su, akwai wadanda ma suka dimauta suka gigita kwarai da gaske, kuma hukumar Saudiyya duk ta kula da irin wadannan Alhazzai kuma an basu tallafin da ya kamata kuma an salami kowa ya tafi gida cikin namu mutanen’’ Ambasada kunbi dukkan masaukin alhazzan Najeriya kuka tabbatar kowanne na cikin koshin lafiya ko ko ta wane hanya kuka gane cewa ba wani dan Najeriya da wannan abu ya rutsa dashi? ‘’Dama duk lokacin da alhaji yazo nan ko a makka ko Madina ko ina ma yake , a ko wane lokaci akwai ido akan sa tunda anan mutum ba a gida yake ba, don haka wajibi a kowane lokaci cikin awa 24 akwai jamiai da ke tare dashi akwai na jihohi akwai na hukumar Alhazai, akwai jamian ofishin jakadanci da ako wane lokaci suke aiki suke sa ido akan halin da alhaji yake ciki’’

'Fina-finan 'Hausa indiya' satar fasaha ne'


Shugaban hukumar tace fina finai ta jihar Kano da ke Najeriya, Sama'ila Na abba Afakallah, ya ce fina-finan Indiya da aka fassara su zuwa harshen Hausa ba bisa ka'ida, tamkar satar fasaha ce. Afakallah ya shaida wa BBC cewa ya kamata masu fassara fina finan su bi doka da tsari na duniya, ciki har da samun izinin hakkin mallakar fina finan gabanin fassara su, yana mai cewa amma ba sa yi. A cewar sa, daga yanzu, hukumarsa ba za ta sake amincewa da duk wani fim da aka fassara daga Indiya ko Amurka, da sauran harsuna ba, sai ta tabbatar cewa wadanda suka fassara su, sun bi ka'idoji. Fina-finan Indiya da ake fassara su zuwa harshen Hausa suna kara farin jini a Najeria, suna kuma barazana ta fuskar kasuwanci ga fina finan Hausa, Kannywood.

Kaza marar kai a Amurka


Kimanin shekaru 70 da suka gabata, wani manomi a garin Colarado na kasar Amurka ya yanke kan wata kaza kuma ta ki mutuwa. Kazar wacce ake kira Mike ta rayu har watanni 18 kuma ta yi fice sosai. Amma ya ya aka yi ta dade a raye ba tare da kai ba ? in ji Chris Stokel-Walker. A ranar 10 ga watan Satumbar shekarar 1945, Lloyd Olsen da matarsa Clara suna yanka kaji a gonarsu da ke garin Fruita a Colarado. Olsen yana yanka kajin, matarsa kuma tana wanke su. Amma daya daga cikin kajin, kimanin 50 din da suke shan wuka a hannun Olsen a ranar sai ta ba da mamaki. A cewar jikan wadannan ma'aurata Troy Waters, wanda shi ma manonmi a garin Fruita, "Bayan sun kammala yanka kajin sai suka gano wata guda daya da bata mutu ba, ta kuma tashi ta ci gaba da tafiya." Kazar ta ari takalmin kare ta zura da gudu kuma ba ta tsaya ba. Christa Waters matar Troy ta kara da cewa "A wannan daren dai sai aka ajiye kazar a cikin wani tsohon akwati da ake ajiyar Tuffah watau Apple a gonar, da gari ya waye ko da Lloyd Olsen ya fito don ya duba halin da ake ciki, sai kawai ya ga kazar nan har a lokacin ba ta mutu ba. Wannan na daga cikin tarihin abin al'ajabi da ya taba faruwa da zuri'armu." Troy dai ya samu wannan labari ne lokacin da yake yaro, lokacin da tsufa ya cimma kakansa ya zo yake zama da iyalan jikan nasa. Dakin Troy na kallon dakin da kakan nasa yake, kuma da yake tsohon ba ya samun bacci sosai, ya kan shafe tsawon sa'o'i yana zuba zance. Troy ya ci gaba da cewa "Ya dauki yankakkun kajin domin ya sayar da su a 'yan kaji, ya tafi da zakaransa - kuma a wancan lokacin yana amfani da doki da kuma mota kirar wagon. Ya dauki kazar ya tafi da ita ya kuma fara cewa mutane in har za su bashi giya ko wani abu to zai nuna musu kazar da an fille mata kai amma har yanzu tana da rai." Zancen wannan kaza mai ban al'ajabi ya bazu tamkar wutar daji a garin Fruita. "Wasa a bainar jama'a" Wata jarida ta tura wakilinta domin ya tattauna da Olsen, makonni biyu bayan da wani mai shirya wasanni a bainar jama'a Hope Wade, ya taho tun daga garin Utah kimanin kilomita 300 domin ya ga kazar. Ya zo musu da wata shawara, inda ya ce su dauki kazar su yi wasa a bainar jama'a don su sami kudi. Troy ya ce "gashi kuwa a wancan lokacin shekarun 1940, 'yar karamar gona kawai muka mallaka, suna faman fafutuka." Da farko sun fara da ziyartar garin Salt Lake City da kuma jami'ar garin Utah, inda aka yi ta yin gwaje-gwaje da batira a kan kazar. An yi ta jita-jitar cewa masana kimiyya na jami'ar sun cire kawunan kaji da dama domin su ga ko za su rayu. A wannan lokaci ne mujallar Life ta yi fice sosai a kan labarin kaza mai ban al'ajabi mai rai babu kai. Daga nan kuma sai Lloyd da Clara da kuma Mike suka tafi Amurka domin yawon shakatawa An ci gaba da bai wa kaza Mike abinci da ruwa ta inda ake zurara mata ta makogwaro. A daren da Mike ta mutu, sun farka ne a dakin kwanansu na otal suka ji tana shakuwa. Kafin su yi kokarin yin wani abu har Mike ta mutu. Wani kwararre a harkar kaji Dr Tom Smulders, ya ce ya gano dalilin da yasa Mike bata yi saurin mutuwa ba, saboda bata zubar da jini sosai ba a lokacin da aka yanka ta.

Kamaru: Boko Haram sun kashe mutane


A Kamaru hare-haren 'yan ƙunar baƙin wake sun kashe mutane 10, yayin da wasu da dama suka jikkata a garin Kolofata. Ana kyautata zaton cewa 'yan Boko Haram ne suka kai harin. Wannan dai ba shi ne karon farko da kungiyar Boko Haram ta kai harin garin na Kolofata wanda shi ne mahaifar Mataimakin Firiya Ministan Kamarun Amadou Ali. Bayanai sun ce Gwamnan Lardin arewa mai nisa Mijinyawa Bakary ya je garin na Kolofata domin gane wa idanunsa abin da ya faru. Jiya ma dai an yi bata kashi a tsakanin dakarun tsaro da 'yan kungiyar Boko Haram a garin Balgaram na karamar Hukumar Hile Alifa inda jami'an tsaron suka kashe 'yan kungiyar Boko Haram uku.

Shaikh Dahiru Bauchi Ya Yaba da Salon Mulkin Buhari


Mai wa'azin addinin musulunci Shaik Usman Bauchi yace a kwanaki dari na farkon mulkin Buhari an samu takawa kungiyar Boko Haram birki Shaikh Dahiru Usman Bauchi yace an kuma samu inganta rayuwar 'yan kasa tare da yaki da cin hanci da rashawa. Cikin kwanaki dari Allah ya nunawa al'ummar Najeriya alamun cin nasara na zaman lafiya. Kafin wannan lokacin yawancin yankunan jihohin Yobe, Borno da Adamawa suna hannun 'yan Boko Haram ne amma yanzu an kwatosu. 'Yan Boko Haram sun yadu sosai saboda a rana daya sun kashe mutane fiye da dubu biyu a Baga suka cigaba da sarafa bom kusa da Ashaka kana suna kai hare hare Nafada da Bajoga da Gombe da Azare. Har cikin Masallacin Jumma'a na Kano sun kai hari. Amma cikin kwanaki dari da Buhari ya kama mulki Allah ya kawar dasu an zauna lafiya. Yanzu 'yan Boko Haram basu da karfin kai hari saidai su ne ake kaiwa hari yanzu. Saboda nasarar da Allah ya bayar suke gode mashi. Allah kuma ya bada lafiya da zaman lafiya d kwanciyar hankali. Shaik Dahiru Bauchi bayan ya yi addu'a sai yace dalilin tara taron malamai ke nan domin a yiwa Allah godiya ta musamman.Ya godewa malaman da suka kasance a wurin addu'an tare da malaman da suka zauna garuruwansu ko kauyukansu amma suka yi addu'a. Da ya amsa tambaya akan salon mulkin Buhari Shaik Bauchi yace shugaban na yaki da cin hanci da rashawa kuma ana yi masa addu'a Allah ya bashi nasara ya kuma ba kasar zaman lafiya ta kowace hanya. Ya ce Allah ya sa a maido da kudaden da aka kwashe domin an wawuresu an kaisu wasu wurare kafin ya kama mulki.

Sabbin Gwamnoni Sun Fara Ciwo Bashi


Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima da na Bauchi Muhammed Abdullahi Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan Benue Samuel Ortom, a wata ziyara da suka kaiwa mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo See comments Share Wani kwararre a harkan tattalin arziki a Najeriya , Yushau Aliyu yayi gargadi. ‘’Bashi wanda aka ciwo kuma ba tabbatar da abinda akayi da bashin ba, kuma aka shiga matsala gwamnati bata iya biyan albashi, shine kaskantaccen yanayi da gwamnati zata samu kanta, akan ciwo basussuka ne domin ayi manyan ayyuka da suka zama wajibi ayi su, idan a yanayin da tattalin arziki ke tafiya, idan wannan jihar ta ciwo waccan ta ciwo haka ita gwamnatin tarayya taje ta ciwo bashin akan harkokin tsaro wannan yana da girma tunda kasafin kudin kasar wanda akayi wa gibi ne da yawa, duk gibin da suka shiga cikin kasafin kudi tunda a zahirin gaskiya duk kasafin kudin da aka yi ana yinsa ne a bisa kididdigar abinda gwamnati zata iya samu na kudaden shigan ta.Yin haka ana jefa tattalin arzikin jihohi cikin rudani, kuma gwamnonin ba zau fita cikin rudani ba, haka kuma ana kara jefa tattalin arzikin kasar cikin rudani sabo da irin abinda ya fara bayyana duk irin cin basussukan da ake yi a Najeriya wanda kanfanin J T Morgan shi ya fara sawa kasar takunkunmi aka cire ma daga jerin wadanda za a yi baiwa bashi sabo da ana duba yanayin halin da tattalin kasar yake.’’ Shima tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Abdul kadir Balarabe Musa masani harkokin tattalin kasa yace matsalar Najeriya ba wai rashin kudi bane wanda zaisa ta rika cin bashi. Ga dai abinda tsohon gwamnan ke cewa. ‘’Akwai kudin Najeriya bata cikin matsalar rashin kudi da zata rika cin bashi matsalan Najeriya shine banna, shine kawai matsalar Najeriya.’’

An Yaba Da Sakamakon Jarabawan Sakandare


Yara suna karatu a karkashin bishiya a sansanin yan gudun hijira a garinMaiduguri See comments Share A taron manema labarai babban magatakardan hukumar a Najeriya Farfesa Abdulrasheed Garba yace sakamakon ya nuna sama da kashi 68 na wadanda suka rubuta jarabawan sun samu nasarar da ake bukata a darasin turanci da lissafi. Wanda wannan ya nuna cewa jarabawar ta bana an samu ci gaba. Farfesa Abdulraseed Garba yace akwai dabarun da hukumar tayi a lokacin jarabawar. ‘’Abinda muka yi shine muka tabbatar cewa duk tambayar da za ayi to ta fito daga cikin abubuwan da aka amince a koyar a makarantun sakandare, wannan yasa muka samar da dangantaka tsakanin hukumar ta NECO da hukumar NRDC, Wannan hukumar ta NDRC ita ce keda allhakin fitar da jadawalin koyarwa’’ A wannan shekarar kuma satar jarabawar bai kai na shekar bara ba. ‘’Labari mai dadi shine magudin da aka samu a wannan shekar bai kai na bara ba domin duk dabarar da kayi sai ka samu magudi amma wanna shekarar bai kai na bara ba, duk da haka mun kakkama an tantance kuma an zakulo wadanda suke da laifi da yawa an soke sakamakon su.’’ Sai dai ya zuwa wannan lokaci hukumar ta NECO tace tana bin wasu jihohi bashin kudin jarabawan su da basu biya ba, kamar yadda Farfesa Abdulrasheed yayi Karin bayani.

Masu Dakon Kaya Sun Tafi Yajin Aiki A Lagos


Matuka manyan motocin dakon kaya suka cika kan manyan hanyoyin faransa domin nuna rashin amincewarsu da shirin garambawul din fansho. See comments Share Masu manyan motoci wanda ke dakon kaya sun fara yajin aiki a birnin lagos domin adawa da dokara hana zirga zirga a titunan birnin daga karfe 6 na safiya zuwa 9 na dare. Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar Lagos ta yiwa masu motocin dakon kaya a birnin cewa su kiyaye hanyoyin birnin karfe 6 na safiya zuwa karfe 9 na dare. Uwar kungiyar masu motocin dakon kayan sun fara wani yajin aiki yajin aikin da sai baba ta gani, domin tilastawa gwamnatin jihar janye wannan umarni nata. Yanzu haka dai harkokin yau da kullum na neman tsayawa cik a babbar tashar jiragen ruwa na kasar inda akasarin masu dakon kayan ke dauko kayansu zuwa wasu sassa daban daban na Najeriya. wannan lamari ya shafi masu hada hadar harkar gwari a birnin na Lagos, al’amarin da ka iya tada farashin kayayyakin saye da sayarwa dama na kasuwanni daban daban dake jihar dama wasu sassa na tarayyar Najeriya. Mataimakin shugaban masu dakon kaya a jihar lagos Alhaji Abdullahi Jiji, yace “aikin mu ma da rana ya aka kare ballan tana ace daga karfe tara na dare zuwa karfe shida na safe, sau dayawa ana kwace musu motoci da kaya ballantana da daddare. Kuma ba zamu iya aiki a wannan lokacin ba.” Suma masu amfana da dagon da motocin keyi sun yi kira ga gwamnatin jihar Lagos ne da ta duba wannan doka da nufin sassauta shi Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibril, ya halarci taron satantawa da yan kungiyar da kuma kwamishinan yansanda inda aka tashi taron ba tare da matsayi ba.

Jam'iyar PDP A JIhar Bauchi Ta kori Shugabanta


Jam'iyar PDP da ta sha kaye a jihar Bauchi ta dauki matakin gyara kura kurai da tace an tafka da ya janyo mata faduwa zabe bara,. Ta kuma sauke wadansu shugabannin jam'iyar tare da barazanar kaisu gaban hukumar EFCC Jam’iyar adawa ta PDP a jihar Bauchin Najeriya ta gudanar da garambawul da ya kai ga tsige shugaban jam’iyar da sakataren jihar, da kuma zaben shugabannin wucin gadi tare da barazanar yiwuwar sa bakin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC. Mataimakin shugaban jam’iyar kuma dan kwamitin zartaswa Salihu Ya’u Nabardo ya yiwa wakilinmu Abdulwahab Mohammed karin haske dangane da batun.

Gungun mahara ya matsawa kamfanoni a intanet


Wani gungun mahara masu kwace ta intanet ya sa Bankuna da kafofin yada labarai da kamfanonin kera manhajar wasanni a gaba. Gungun ya sa su a gaba ne ta hanyar yi musu barazar su biya su wasu kudadade ko su lalata shafukan na kasuwancinsu na intanet. A cikin wani rahoto da Akamai wani kamfanin intanet ya fitar, ya ce a watanni 10 da suka wuce gungun ya kai wa masu ciniki da su hari har sau 141 a intanet Gungun maharar ta intanet da ake kira DD4BC ya yi barazanar makare rumbun ajiyar bayanan kamfanin idan bai biya fansar kudin intanet bitcoin 50 kimanin £8,000 ba. Gungun na kai hari a shafukan intanet ta hanyar cika shafin wanda ya ke hari da ambaliyar gigabits 56 na bayanai a dakika 1. A cewar rahoton Akamai gungun maharan na DD4BC na nan tun cikin watan Satumba na 2014 sai dai a kwanakin nan ne ya matsa kaimi da kai hari akan harkokin kasuwanci a intanet. Harkokin hada-hadar kudi na daya daga cikin inda gungun ya matsawa lamba ta hanyar kwace da cin zarafi da batanci da kuma sa a ji kunya a idon jama'a a cewar Stuart Scholly shugaban tsaro na kamfanin Akamai.