Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya ki bai wa
mutane da dama mukamin ministoci ne saboda ana zargin
suna da hannu a karbar hanci da rashawa.
Buhari ya shaida wa BBC cewa duk da haka zai nada ministoci a
watan Satumba da muke ciki, kana ya ci gaba da gudanar da
binciken wasu mutanen.
A cewar sa, "Akwai wadanda ya kamata a ba su [mukaman
ministoci] saboda sun san ayyukan; ko ayyukan kudi, ko ayyukan
sha'anin mai, ko tsarin mulki; amma sai ka ga ta wata hanya --
da sanin su, ko ba da sanin su ba -- sai ka ga an ja su [cikin
rashawa]. Daukar irin wadannan shi ne masifar Dan wanzan; ya
zamana kai ka dauko mutum, ka yi zaton mutumin kirki ne,
amma wasu na can suna juya shi".
Shugaba Buhari ya ce abubuwan da idanunsa suka gani game da
barnar da aka yi wa Najeriya ba kanana ba ne, yana mai cewa
dole ne mutanen da zai bai wa mukaman su zama adalai.
Shugaban na Najeriya ya kare matakin da ya dauka na nada
mutanen da ke kusa da shi a matsayin manyan jami'an
gwamnatinsa, yana mai cewa tsarin mulki ya ba shi damar nada
na kurkusa da shi a kan mukaman da ba sa bukatar amincewar
Majalisar Dattawa kafin a nada su. BBCHAUSA
Translate site
Tuesday, 8 September 2015
Ba zan nada mutanen da ke da tabon sata ba — Buhari
Subscribe to:
Posts (Atom)