Samar da hanyoyin shiga intanet masu sauri a wayoyin salula a Afrika da Indiya za su kauce wa hanyoyin da aka saba bi wajen bunkasa tattalin arziki.
Hanyoyin shiga intanet masu sauri a wayoyin salula sun sa Afrika da Indiya samun ci gaba cikin hanzari.
Gwamnatoci a wadannan kasashe sun hakikance cewa amfani da hanyar sadarwa ta intanet na 4G ya fi bunkasa harkokin kasuwanci fiye da hanyoyin sadarwa da aka fi sani a da.
Wani dan Najeriya mai yada labarai ta intanet, Yomi Adegboye, ya ce ci gaban fasahar zamani ya kawo bunkasar kasuwanci sosai.
Mista Adegboye ya kara da cewa, "A yanzu ina iya yin abubuwa da dama da intanet cikin kankanen lokaci ba kamar a baya ba. Samun hanyar sadarwa ta intanet mai sauri na nufin mun yi nisa a ci gaba na zamani."
Ya ce ana iya sauko da abubuwa daga intanet cikin sauki, kuma hakan yana kara wa abokan cinikinsu kwarin gwiwa.
Mista Adegboye na daya daga cikin mutane na farko da suka fara cin moriyar hanyar sadarwa ta intanet na 4G a Najeriya da Afrika.
"Bambanci karara"
Amma ko mene ne dalilin da ya sa za a tafi kai tsaye zuwa hanyoyin intanet ta 4G a nahiyar da wurare da dama ba su da hanyoyin intanet na 3G ko 2G?
Shugabar kamfanin sadarwa na Smile Group, Irene Charnley, ta ce dalilin hakan shi ne saboda amfani da 4G ya fi sauri da kuma samar da biyan bukata.
"Samuwar Intanet a Indiya"
A Indiya kuwa, Firai minista Narendra Modi yana bai wa harkokin intanet muhimmanci karkashin wani shiri da ya bullo da shi mai taken "Digital India," da zummar cewa hakan zai taimaka wajen zamanantar da harkokin kowanne bangare na kasar, kama daga harkar ilimi da lafiya da samar da abinci da kuma kere-kere.
Masu amfani da wayar salula kimanin miliyan 950 a kasar sun fi amfani da wayoyin salularsu ne don yin kira, saboda har yanzu hanyar sadarwa ta intanet bata da sauri a kasar.
Shugaban wani kamfanin sadarwa na Culture Machine, Sameer Pitalwalla, ya ce yana kokarin ganin ya gano hanyar da za a yi domin intanet ya dinga sauri yadda ake so.
Amma a yayin da biranen Indiya da na Afrika ke cin moriyar amfani da hanyar intanet na 4G, al'ummar kauyukansu na ganin kamar an bar su a baya saboda masu samar da hanyoyin inatent sun fi mai da hankali ga bunkasa birane.