Translate site

Wednesday 30 September 2015

Yan Boko Haram na zuba guba a ruwa


Ana zargin mayakan Boko Haram na zuba guba a rijiyoyi da rafuka a wasu kauyukan da aka kore su a jihar Borno da ke arewacin Nigeria. Rundunar sojin Nigeria a Maiduguri ta ce bayanan da ta samu sun nuna cewar 'yan Boko Haram na aikata wannan ta'asar a garuruwan da dakaru suka kore su. Wata sanarwa da mai magana da yawun soji a Maiduguri, Kanar Tukur Gusau ya fitar, ta ce yanzu haka akwai shanun da suka mutu sakamakon shan ruwan wani rafi da aka saka guba. Sanarwar ta bukaci al'ummar yankin su guji shan ruwan da ba a tantance inda aka debo shi ba, saboda gudun fadawa cikin hadari. A cewar rundunar sojin akwai rafin da aka zuba guba a cikinsa a kauyen Kangallam da ke kan hanyar Marte zuwa Abadam. Rundunar sojin ta ce za ta ci gaba da kokari domin kawar da 'yan Boko Haram daga maboyarsu

Ni zan rike ma'aikatar man fetur — Buhari


Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa yana da aniyyar shi da kansa ya ja ragamar ma'aikatar man fetur ta kasar yayin da yake ci gaba da yaki da karbar hanci da rashawa. Kawo yanzu dai Shugaba Buhari bai sanar da sunayen ministocinsa ba tun bayan da aka rantsar da shi a watan Mayun wannan shekarar. A kwanakin baya ne dai shugaban kasar ya sha alwashin bankado makuden kudaden da aka sace a bangaren albarkatun man fetur na kasar, bangaren da ke samar da kashi 70 cikin 100 na kudaden da gwamnatin kasar ke samu. Nan gaba kadan ne dai ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai mika sunayen ministocinsa ga Majalisar dattawan kasar domin a tantance su.