cikin 37 da shugaba Muhammadu Buhari ya ke son ya
nada a matsayin ministoci.
Majalisar karkashin jagorancin, Sanata Abubakar
Bukola Saraki ta gayyaci mutanen daya bayan daya
domin amsa tambayoyi kan rayuwarsu da kuma irin
ayyukan da suka yi.
An soma ne da Sanata Udoma Udo Udoma daga jihar
Akwa Ibom wanda bayan ya gabatar da kansa sai
aka ba shi damar ya rusunawa 'yan majalisar sannan
ya kama gabansa.
Sauran wadanda aka tantance a zaman farko a ranar
Talata sun hada da; Kayode Fayemi daga jihar Ekiti,
da Audu Ogbeh daga jihar Benue da Ogbonayya Onu
daga jihar Abia da kuma Osagie Ohanire daga jihar
Edo.
Tsohon babban hafsan sojin kasa na Nigeria, Laftar
Janar AbdulRahman Dambazau daga jihar Kano da
Kakakin jam'iyyar APC na kasa, Alhaji Lai
Muhammed da kuma Hajiya Amina Mohammed 'yar
jihar Gombe na daga cikin mutanen da suka bayyana
gaban majalisar.
Injiniya Sulaiman Adamu daga jihar Jigawa da kuma
Alhaji Ibrahim Usman Jibrin daga jihar Nasarawa su
ne mutane na karshe da suka bayyana gaban
majalisar kafin ta dage zamanta.
Ana sa ran a ranar Laraba majalisar dattawan za ta
koma zamanta domin ci gaba da tantance mutanen
da ake son a nada ministocin.
Jerin wadanda aka tantance:
Sanata Udoma Udo Udoma daga jihar Akwa Ibom
Kayode Fayemi daga jihar Ekiti
Audu Ogbeh daga jihar Benue
Ogbonayya Onu daga jihar Abia
Osagie Ohanire daga jihar Edo
Laftar Janar AbdulRahman Dambazau daga jihar
Kano
Alhaji Lai Muhammed daga jihar Kwara
Hajiya Amina Mohammed daga jihar Gombe
Injiniya Sulaiman Adamu daga jihar Jigawa
Alhaji Ibrahim Usman Jibrin daga jihar Nasara