Translate site

Monday, 14 September 2015

Za a rage ma'aikatan jirgi saboda kibarsu


Kamfanin jiragen sama na Indiya yana shirin rage ma'aikatan jirgi su kimanin 125, saboda a cewarsa sun yi kiba da yawa. Wani jami'in jiragen sama na Indiya ya shaida wa BBC cewa an dauki matakin ne saboda bin dokar da hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta bullo da ita wadda ta shafi nauyin jiki a bara. Jami'in ya ce kamfanin jiragen saman ya gargadi ma'aikatansa kimanin 600 su rage kiba, amma har yanzu 125 daga cikinsu ba su rage kibar yadda ake bukata ba. Ya ce an lura cewar ma'aikatan cikin jirgi masu kiba ba sa iya taimakawa yadda ya kamata a lokacin da wani al'amari da ke bukatar taimakon gaggawa ya faru.

Buhari zai gana da shugaban Faransa


Ana sa ran a shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da takwaransa na Faransa Francois Hollande a ranar Litinin da daddare a kan tsaro da kasuwanci. Shugaba Buhari ya sauka a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Litinin din a ziyarar kwanaki uku da zai yi a kasar. Shugaban ya samu tarba daga manyan jami'an gwamnatin kasar. Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna a kan yadda kasashen biyu za su hada gwiwa domin shawo kan matsalolin tsaro da inganta kasuwanci. Kazalika, Shugaba Buhari zai gana da ministocin tsaro da kudi da tattalin da kasashen waje na kasar ta Faransa. Haka kuma, zai gana da jakadun kasashen Afirka da ke Faransa da 'yan Najeriya da ke kasar. Kasar ta Faransa dai ta sha alwashin hada gwiwa da Najeriya domin murkushe kungiyar Boko Haram, wadda ta addabi Najeriya da makwabtanta irin su Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi, kasashen da ke da alaka da kut-da-kut da Faransa. Shugaba Buhari ya yi tafiyar ne tare da mai ba shi shawara a kan tsaro Manjo-Janar Babagana Monguno da Manyan Sakatarorin ma'aikatun tsaro da kudi da aikin gona da harkokin kasashen waje da masana'antu.

YNS english class Funny


Berry funny wach it