Translate site

Wednesday 14 October 2015

Dalibi ya saye Kamfanin Google na minti 1


Wani kuskure da masu gudanarwar katafaren kamfanin binciken intanet Google.com ya yi, ya sa wani dalibi Sanmay Ved ya saye kamfanin a ranar 29 na Satumba.

Dalibin Mista Sanmy Ved mai karatun digirin digirgir na MBA a wata kwaleji a Amurka, ya karbe ikon gudanar da Google.com na tsawon minti guda kafin kamfanin ya farga ya kuma soke cinikin.

Mista Ved ya ba da labarin yadda abin ya faru a shafinsa na sada zumunta na LinkedIn a intanet a inda yake cewa ya jima yana sa ido akan shafukan da ke da danganta da kamfanin Google na tsawon lokaci saboda ya taba aiki da shi.

A safiyar ranar 29 na watan Satumba ne ya gano wata sanarwar sayar da kamfanin a shafin kamfanin Google a intanet a yayin da yake ziyartar shafukan saye da sayarwa na Google din.

Ganin haka sai ya biya dala 12 farashin da ake nema ta hanyar katin biyan kudi, kuma nan take aka sayar masa da kamfanin Google.com

Ya na samun wasikar email din da ta tabbatar masa da mallakin kamfanin, sai Mista Veb ya soma samun wasikun kamfanin da su ka kamata su je ga hukumoni da kuma masu gudanar da kamfanin.

Jim kadan kuma sai ya samu wata wasikar da ta soke cinikin daga shafin na saye da sayarwar kamfanin tare da bayanin cewa ba zai mallaki kamfanin ba saboda wani ya riga ya yi rijistarsa, aka kuma dawo masa da kudinsa.

Faruwar hakan ta sa kamfanin ya farga da wannan nakasu, hakan ya sa masu kula da tsaro na kamfanin su ka yi wa Mista Ved din kyauta saboda gano wannan nakasun na saye da sayarwar kamfanin.

Daga baya Mista Ved ya mikawa hukomomin kamfanin dinbin sakonnin email din da ya samu a yayin da ya ke mallakin sa. Ya kuma mika kyautar kudin da Google din ya ba shi ga wata gidauniyar inganta ilimi ta India, da jin haka kuwa Kamfanin ya ninka kyautar kudin.

Twitter zai rage ma'aikata saboda gyare- gyare


Kamfanin Twitter ya ce zai rage guraben ayyuka 336, na ma'aikatansa a wani bangare na sake yin gyare- gyare ga harkokin kasuwancinsa.

Rage guraben ayyukan zai ci tsakanin Dala miliyan 10 da Dala miliyan 20 na kudaden sallama.

Yayinda gyare- gyaren zai ci tsakanin Dala miliyan 5 da kuma Dala miliyan 15 in ji kamfanin Tweeter.

Hannayen jari a Twitter sun tashi zuwa kashi 2% bayan sanarwar.

Wannan mataki na zuwa ne wasu 'yan kwanaki bayan da aka tabbatarwa da Jack Dorsey kujerar babban jami'in gudanarwa na dindindin na Kamfanin.

Ya rike mukamin shugaban kamfanin na rikon kwarya har tsawon watanni uku bayan da Dick Costolo ya sauka a ranar 1 ga watan Yuli.

A wata wasika da ya aike wa ma'aikatan Tweeter, Mr Dorsey ya rubuta cewa: ' Mun dauki shawara mai wahalar gaske-mu na shirin sallamar mutane 336 daga kamfani'.

'Za mu yi hakan ne tare da matukar mutunta kowa' in ji Dorsey