Translate site
Thursday, 3 September 2015
Musha Dariya:- Banbi Ta Layin Yanwutaba
writing by:- abdullahi saleh muhd
Wani maigida yashigo gida a fusace cikin fushi sai matarsa sce dashi megida barka da zuwa, daga ina ? budar bakin mai gida sai yace daga lahira nake, sai matarsa tace Allah sarki kagano babata da babana kuwa sai yace BANBI TA LAYIN YAN WUTABA.
Musha Dariya:- Duk irinku ne kuke ja mana zagi a gari
Parent Category: Mu Sha Dariya
Category: Mu Sha Dariya
Published on Friday, 28 August 2015 12:36
Written by Abdullahi Saleh Muhd
Hits: 902
Wani mahaukaci ne ya fito yawo kasuwa ba wando ba riga! Kawai sai ga wani mahaukaci shi ma ya zo sai wannan mahaukaci ya hango dayan, ba riga ba wando sai ya kamo hannunsa ya kwada mai mari. Ya ce duk irinku ne kuke ja mana zagi a gari. Sai ya kwabe kayan jikinsa ya ba shi ya sa, sh ikuma ya yi tafiyarsa tsirara. Shin a cikinsu waya fi wani hauka? abdullahi saleh muhd 08144454538
Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da imel (3)
Category: Kimiyya da fasaha Published on Friday, 27 March 2015
00:00 Written by Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq) Hits:
2148
Assalamu alaikum, yaya aiki? Na ga wata waya mai suna:
Tecno F7, ina so in saya, amma don Allah ina so a ba ni
shawara kafin nan. Kuma akwai wata waya nokia N1, an ce
ba ta da SIM da kuma rediyo shin gaskia ne? Na gode - Isa
Salisu
Wa alaikumus salam, aiki Alhamdulillah. Shawara dangane da
Tecno F7, ban san me kafi bukata a jikin waya ba balle in san
irin shawarar da zan ba ka. A tare da haka, waya ce mai kyau,
tana dauke da babbar manhajar Android, mizanin ma’adanar waya
4GB, da ma’adanar wucin-gadi (RAM) 1GB. Sannan kaifin kemara
dinta 8MP ne. Tana da kemara a goshinta mai dauke da kaifin
2MP. Na’urar sarrafa umarninta (Processor) na da inganci.
Sannan za ka iya sa mata karin ma’adana ta MMC har zuwa 32GB.
A bangaren Nokia N1 kuma, kamar yadda ka ji, ba wayar salula
ba ce, domin ba ta dauke da na’urar siginar rediyo, balle katin
SIM. Na’urar Sarrafa bayanai ce. Tana dauke da tsarin sadarwa
na wayar iska, wato Wireless LAN (WLAN) na zamani. Ma’adanarta
da ta zo da ita ta kai mizani 32GB, sannan ma’adanar wucin-gadi
(RAM) 2GB ce. A takaice dai na’ura ce ta sarrafa bayanai da
mu’amala da bayanai, amma ba wayar salula ba ce. Idan kana son
mu’amala da Intanet, da kallon bidiyo da sauraron sauti da
saukar da manhajoji da masarrafai masu kayatarwa da
ilimantarwa, to, za ta iya maka, iya karfin da aka ba ta. Amma
aiwatar da kira ko karban kira, ba da ita ba, wai gada a
makabarta.
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Ko yaushe
muna maka addu’ar fatan alheri dangane da karuwa da kai da
muke yi. Allah saka da alheri. Baban Sadik ina so ka kara wayar
mini da kai ne game da tsarin ‘Google+’. Ta yaya zan aika wa
wani sako ta Google+? Daga Abdulazeez Adamu Fira, Birin-Fulani,
Nafada, Gombe.
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdulazeez. Shafin “Google
+” shafin dandalin abota ne na kamfanin Google Inc dake
Amurka. Yana da kamaiceceniya da Facebook ta wasu bangarori,
amma galibin tsare-tsarensa sun sha bamban da na Facebook.
Idan kana son aika wa mutum sako ta wannan shafi kana iya yi
ta hanyoyi da dama. Hanya ta farko ita ce tura masa sakon kai
tsaye a shafinsa, idan har akwai abota a tsakaninku kenan.
Ma’anar sakon kai tsaye, ita ce: “Pribate Message,” ko “Inbod,”
kamar yadda ake fada a dandalin Facebook. Hanya ta biyu, kana
iya aika masa ta jakar Imel dinsa, wato Gmail kenan. Domin duk
wanda ka gani da shafi a Google +, to lallai yana da adireshin
Gmail. Sabanin shafin Facebook da za ka iya amfani da kowane
irin adireshin Imel ne ko ma lambar waya, a Google + sai ka yi
rajista da manhajar Imel na kamfanin Google mai suna Gmail. Da
zarar ka yi rajista da Gmail, to, kana iya mallakar shafukan
Google da dama, kyauta. Hanya ta uku ita ce, kana iya aika masa
sako ta hanyar shafinsa kai tsaye, ko ka yi ta’aliki kan sakon da
ya rubuta a shafin ko wani abu makamancin hakan. Da fatan ka
gamsu.
Assalamu Alaikum. Na gaida Baban Sadik da irin ayyukan da kake
yi wajen taimakon jama’a ta hanyar karuwa na ilimi. Tambaya
nake da ita. Na farko, ina da kwamfutar tafi-da-gidanka
(Laptop) mai dauke da babbar manhajar “Windows 7.” Ina son in
loda mata nau’in “Windows 8.” Wasu hanyoyi zan bi don tabbatar
da ba a samu matsala ba? Tambaya ta biyu: shin, zan iya sayo
babbar manhajar “Windows 8” irin wanda ‘yan kasuwa suke
sayarwa na loda mata, ba wata matsala? Da fatan zan samu
amsoshinsu. Daga Bilyaminu D Sulaiaman, Bauchi.
Wa alaikumus salam Malam Bilyaminu, da fatan kana lafiya kai
ma. Zan fara da tambayarka ta biyu. Idan na fahimceka sosai,
kana nufin irin wadanda ake sayar da su a kan titunan biranen
kasarmu kenan. Wadannan nau’ukan manhajoji tabbas suna da
kyau a karan kansu, sai dai kuma hanyar da ake bi wajen samar
da su, ina nufin masu sayar da su kenan, haramtacciyar hanya
ce. Shi ya sa idan ma ka saya ka loda wa kwamfutarka, muddin
za ka yi mu’amala da fasahar Intanet a kan wannan babbar
manhaja da ka saya ta wannan hanya, dole kamfanin Microsoft
zai gane. Wannan zai sa ka ga kwamfutar ta fara sanar da kai
cewa: “Wannan babbar manhajar ba ta asali ba ce...” a duk
sadda ka kunna ta. Daga baya ma suna iya hana ka mu’amala da
babbar manhajar; idan ka kunna sai ta kulle kanta, ta ce ka
nemo mai kyau ta asali ka sa.
Hakan ya faru ne saboda masu sayar da su na bin haramtacciyar
hanya ce wajen samar da su da yada su. Su kuma suna samun
kasuwa ne saboda asalin wadanda ake sayarwa na asali daga
kamfanin Microsoft suna da dan karen tsada. Idan kana bukatar
nau’in Windows 7 Starter wanda mutum 1 ko 3 za su iya amfani
da ita, gangariya mai kyua, dole sai ka kashe sama da dubu 30 a
Najeriya! A takaice dai amfani da ire-iren wadannan manhajoji,
duk da lalurar tsadar masu asali ko gangariya, yana dauke da
matsaloli, sannan ba lallai ba ne ka samu biyan bukata
cikakkiya. Wannan shi ne abin da ya kamata ka fahimta a farko.
Dangane da loda wa kwamfutarka wata babbar manhaja bayan
wadda take dauke da ita, wannan shi ake kira “Dual Booting,”
idan guda biyu ne, idan manyan manhajoji uku ne a ce: “Tripple
Booting.” Kafin yin hakan, zai dace ka lura cewa, kowace babbar
manhajar kwamfuta tana da ka’idojin mahalli da take bukatar a
cike su kafin a loda wa kwamfuta ita. Wanann shi ake kira
“System Rekuirements.” Ba kowace kwamfuta mai dauke da
babbar manhajar Windows 7 ake iya loda mata Windows 8 ba, sai
an yi la’akari da tsarinta. Me ye mizanin babbar ma’adanarta,
wato: “Hard Disk Dribe?” me ye mizanin ma’adanar wucin-gadi
(RAM) da take dauke da ita? Sannan meye mizanin na’urar
sarrafa umarni (Processor) da ke kwamfutar? A talakance, ana
bukatar mizanin ma’adana 15GB zuwa 20GB. Ana bukatar mafi
karancin mizanin ma’adanar RAM 1GB zuwa 2GB. Sannan ana
bukatar kwamfutar ta kasance da na’urar Processor 1Ghz zuwa
1.5Ghz. Wannan a talakance kenan.
Idan ka tashi loda mata Windows 8, bayan ka tabbatar da
cancantar mahallin da babbar manhajar za ta zauna a ciki, dole
ne ka raba babbar ma’adanar gida biyu, wannan shi ake kira
“Disk Partitioning.” Idan sauran filin da ke babbar manhajar ya
kai 100GB misali, sai ka yanki 60GB don baiwa Windows 8. Akwai
manhajoji da za ka iya amfani da su wajen yin hakan; wadanda
suke cikin kwamfutarka da wadanda za ka iya saukarwa daga
Intanet. Sai ka kintsa bangaren da ka yanko daga ma’adanar,
wato: “Disk Formatting” kenan. Idan ka gama da wannan
bangare, sai ka sanya faifai ko ma’adanar da ke dauke da babbar
manhajar Windows 8 din, ka kashe kwamfutar ka sake kunna ta.
Idan ta fara kunnuwa, za ta dan dakata idan ta ji alamun faifan
CD/DbD a cikinta, sai ta ce maka: “Press Any Key to Boot from
CD/DbD ROM.” Da zarar ka ga wannan sako, sai ka latsa kowane
maballi daga allon shigar da bayananka, wato “Keyboard” kenan.
Daga nan za ta budo maka ma’adanar kwamfutarka, wato “Hard
Disk Partitions,” ta tambayeka inda kake son loda wannan babbar
manhajar. Ka lura, za ka ga “Local Disk (C) – Windows 7” da
“Disk (D) – sunan da ka ba bangaren...” misali. Ka zabi Disk D,
tunda shi ne bangaren da ka yanko daga uwar ma’adanar. Kada ka
zabi “Local Disk (C),” idan ka yi haka za a goge wannan babbar
manhajar ta Windows 7, don ita ce dauke a ciki. Sai a kula da
kyau. Idan ka zaba, sai ka bar mata sauran ayyuka. Za ta saukar
da dukkan bayanan da take bukata daga wannan faifan CD/DbD
zuwa wani bigire na wucin gadi (Temporary folder) da ke
cikinta. Za ka ga tana sanar da kai cewa: “Loading System
Files...” ko wani abu makamancin hakan.
Da zarar ta gama saukar da bayanan da take bukata, za ta sake
kashe kanta, ta kunna kanta nan take. Kar ka taba ta. Kada ka
yi mata katsalandan; ka bar ta kawai, ita za ta ci gaba da
sarrafa kanta. Tana gama kunnuwa sai ta fara loda babbar
manhajar. Wannan zai dauki lokaci, ya danganci mizani da kuzarin
kwamfutar. Kai dai ka rika lura da bayanan da take bayyanawa a
shafin fuskarta kawai. Za ta kashe ta sake kunna kanta akalla
sau 3, kafin ta je marhalar da za ta nemi bayanai daga wajenka.
Idan ta kai wannan marhala za ka gane, domin abu na farko za
ta bukaci ka zabi kasar da kake. Sai ka gangara kasa wajen
harafin N, ka zabi Najeriya. Sai harshe, sai nau’in tsarin allon
shigar da bayanai (Keyboard Settings). Sai kwanan wata, sai
lokaci...da dai sauran bayanai. Idan ta gama karbar bayanai daga
wajenka ma za ta sake kashe kanta ta kunna kanta. Daga nan za
ta ce maka: “Wait...Setting up your desktop for the first
time...” ko wani sako makamancin wannan. Da zarar ta gama
wannan aiki, sai ta kaika shafin farko, wato: Desktop kenan.
Wannan bayani ne a takaice, a gajarce, a talakance. Idan ba ka
da sanayya kan halayya da tsarin kwamfuta, ka kai wa kwararru
don su yi maka. Ka sanar da su abin da kake so, da yadda kake
son abin ya kasance. Wannan bayani na yi maka ne don ya
haskaka maka hanya. Da fatan ka fahimta kuma ka gamsu.
Salamun alaikum, don Allah ina da tambaya. Da yawa na lura idan
na bude Group a Dandalin Facebook idan aka aika sako, nakan ga
ana cewa: “Mutane kaza sun gani”, wato “20 Seen,” misali. To
don Allah ya ya zan yi in cire wannan sakon sanarwar, don a
daina nuna cewa “20 people saw this?” - Mahmoud Abdullahi
Wa alaikumus salam, Malam Mahmoud, wannan sako da kake gani
daga tsarin shafin ne, kai da kake da Zaure a Dandalin Facebook
ba za ka iya cire shi ba. Kada ka mance, wannan sako wata
hanya ce ta karin sanarwa ga duk wanda ke cikin Zauren. Sannan
hanya ce har wa yau da hukumar Facebook ke bi wajen taya mai
shafin lura da ayyukan dake gudanuwa a zauren. Idan ba ka so,
kuma kai ne da zauren, sai dai ka yi hakuri. Zuwa yanzu dai,
ban san wata hanya (duk da na kwana biyu ban yi nazarin
sababbin tsare-tsaren Facebook ba) da hukumar Facebook suka
tanada don cirewa ko hana wanan sako bayyana ba. Sai dai
watakila nan gaba. Domin a kullum suna aiwatar da sauye-sauye
kan shafin. Ta yiwu nan gaba idan suka samu korafe-korafe da
dama daga wajen jama’a su samar da hanyar cire sakon. Da fatan
ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Allah Ya
kara basira, ameen! Wai don Allah ta ya ya zan bude Laptop dina
da ta kulle; idan na kunna ga abin da take rubutawa: “GRUB
LOADING STAGE 1.5. GRUB LOADING, PLEASE WAIT...” Allah Ya sa a
dace, amen. Daga Nuruddeen Umar, Katsina.
Wa alaikumus salam Malam Nuruddeen, barka da warhaka. Duk da
cewa ba ka yi bayanin hakikanin abin da ya faru ba; wace irin
babbar manhaja ce a kwamfutar? Idan guda biyu ce, wani iri da
wace iri? Sannan me ya faru kafin ka samu wannan sako? Abin
da nake iya fahimta shi ne, kamar kana da manhajojin kwamfuta
nau’i biyu ne a kwamfutar; da Windows, ko dai Windows dP ko
Windows 7. Sannan da babbar manhajar kwamfuta nau’in Linud;
ko dai Backtrack, ko Kali Linud, ko kuma Ubuntu zubi na 8
(bersion 8.04). Sannan, idan zan kara hasashe, watakila kana
son cire nau’in Linud din ce, don komawa kan Windows da ka
saba da ita. A tunanina wanan shi ne kusa da abin da zai iya
kasancewa.
Da farko dai wannan sakon matsala (Error Message) da kake
samu shi ake kira “Error 17” idan nau’in Ubuntu ce. Idan kuma
nau’in OpenSuse ce, ana kiransa “Error 22.” Hanya mafi sauki
wajen warware wannan matsala, in har so kake ka cire wancan
babbar manhaja ta nau’in Linud, wanda sanadiyyar hakan ka kasa
shiga Windows dinka, kana iya amfani da faifan CD/DbD mai
dauke da babbar manhajar nau’in Windows din da kake amfani da
shi, don gyara matsalar. Sai ka sanya faifan da ke dauke da
babbar manhajar a kwamfutarka, ka sake kunna ta. Da zarar ta
ji faifan CD/DbD din a cikinta, za ta yi yunkurin farkawa ta
bangarensa, daga nan sai ka gyara matsalar. Bayan ka gyara
Windows din, sai ka yi amfani da “Windows Partition Manger”
don goge wancan bangaren ma’adanar dake dauke da babbar
manhajar Linud.
Wannan gajeriyar shawara ce wacce na gina ta kan hasashe da na
yi a sama. Idan ba ka da sanayya kan halayya da tsarin
kwamfuta, kana iya kaita wajen masu gyara ka bayyana musu
matsalar, a aikace, don su gyara maka. Da fatan ka fahimta.
Baban Sadik na ji bayaninka akan Facebook yanzu a Sunna Tb.
Amma ina so na fahimci yadda ake bude Group? Sannan mene ne
alakar Youtube da Facebook? - Sa’ed A. Sa’eed
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Sa’eed. Idan kana bukatar
bude shafin Group a Dandalin Facebook, ka je shafinka, ka
gangara kasa kadan daga hagu, za ka ga inda aka rubuta: “Create
Group,” sai ka latsa. Za a kaika inda za ka tsara yadda kake son
shafin ya gudanu. Daga sunan shafin, zuwa maudu’in da za a
rika tattaunawa a ciki, da kuma matsayin kowane mamba wajen
aika sako, da dai sauransu. Dangane da asali da gudanuwa, babu
wata alaka a tsakanin shafin Youtube da Facebook. Abin da ya
hada tsakaninsu kawai shi ne, kasancewarsu shafukan abota ne.
Shafin Youtube na kamfanin Google ne, a daya bangaren kuma,
shafin Facebook na kamfanin Facebook ne, dukkansu a Amurka.
Da fatan ka gamsu.
Motorola ya kirkiro agogon Moto 360
Kamfanin Motorola ya sanar da fitar da sabbin agogonan komai
da ruwanka na zamani mai suna Moto 360 dauke da manhajjar
Android.
Agogonan za su kasance kala biyu inda na farko aka sanya
na'urar GPS don gano wurare a duk lokacin da ba'a hada agogon
da wayar tarho ba.
Kamfanin ya ce za a ba masu sha'awar agogon damar zana irin
yadda suke son fasalin agogon su a duk lokacin da suka yi odar
agogon daga kamfani.Motorola ya fitar da sabbin agogunan ne a kasuwar baje kolin
kayayyakin fasaha a Berlin.
Farashin kowane agogo ya danganta daga irin kirar sa, amma
farashin zai fara ne daga £229 idan aka fara sayar da agogonan
nan gaba a watan Satumba.
Subscribe to:
Posts (Atom)