Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta ce babu ko daya daga cikin mahajjatan kasar da ya rasu sakamakon hadarin rikitowar babbar kugiyar daukan kayan gine-gine akan mahajjata a Saudiya.
Sai dai shugaban hukumar, Alhaji Abdullahi Muktar wanda ya sanar da hakan ya ce mutane uku ne 'yan Najeriya suka jikkata sakamakon hadarin.
Ya ce mutanen sun hada da biyu maza da daya mace, sannan mahajjata ne daga jihohin Kaduna da Gombe.