Translate site

Wednesday, 9 September 2015

Ya kashe kansa da ’ya’yansa 2 don an kore shi daga aiki


Wani uba ya kashe ’ya’yansa biyu kafin daga bisani ya harbi kansa da bindiga domin an sallame shi daga aiki, kamar yadda jaridar Daily Mail ta bayyana. Mutumin mai suna, Julian Roary, mai shekara 47 da haihuwa, wanda shi ne mahaifin ’ya’yan biyu: guda dan shekara 10, guda kuma dan shekara 12, ya aikata wannan danyen aikin ne a gidansa da ke garin Baltimore na kasar Amurka. Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ya ce Mista Julian yana cikin wani yanayi ne bayan da ya rasa aikinsa kuma bai kai ga samun wani abin yi ba, a daidai lokacin da al’amarin ya faru. Kodayake, an ce bai bayyana dalilin da ya sa shi yin hakan ba a wasiyyar da ya bari. Mista Julian da babban dansa a nan take dai suka rasu, amma karamin dansa sai bayan da aka kai shi asibiti ne ya cika. Bazawarar marigayin ta bayyana yaran da wadanda kowa zai yi alfahari da su. Ta ce tun da babansu ya rasa aikinsa a shekarar 2009 ya shiga cikin wani mawuyacin hali. “A kullum yakan shiga damuwa sosai idan matsalolin kudi musamman na sauke nauyin iyalinsa suka bijiro masa,” inji ta.

Alajabi:- ‘An gano kur’ani mafi dadewa a duniya’


A shekaran jiya Laraba ne masu bincike a Jami’ar Birmingham da ke kasar Biritaniya suka ce sun gano takardun Al-kur’ani ( Bugun Hannu) da suka fi tsufa a duniya, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito. Masu binciken sun ce wani nazarin kimiyya da suka yi a kan takardun sun nuna cewa an wallafa su ne fiye da shekaru 1,370 da suka wuce. Sun kuma ce takardun suna ajiye ne tare da wasu littattafan yankunan Gabas-ta-Tsakiya, inda bincike ya nuna cewa wani masanin tarihi dan asalin kasar Iraki, mai suna Alphonse Mingana, ne ya kai takardun jami’ar a shekarun 1920. An ce mai yiwuwa mutumin da ya rubuta Al-kur’anin ya taba haduwa da Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ko kuwa ya taba jinsa lokacin da yake wa’azi. Wani masani kan dakunan adana littattafai a Birtaniya, Dokta Muhammad Isa Waley ya ce, “wannan wani abu ne da Musulmi za su yi farin ciki da shi”

China ta gina hanyar da bam ba ya fasawa


kasar China ta shinfida kwalta, wadda bam ba zai iya fasata ba, a kan wata babbar hanya da ke isa Dandalin Tiananmen Skuare da ke birnin Beijing, kamar yadda jaridar kasar mai suna Shenzhen Ebening Post ta wallafa. kasar ta gudanar da aikin ne gabanin wani babban faretin sojin da za a yi a dandalin a watan Satumbar bana. An shinfida wani abu a karkashin kwaltar, hakan ya sanya kwaltar ta kara kauri da kusan mita guda. Har ila yau, an dasa abubuwan da suke samar da rigakafi daga fashewar bam ciki har da kankare. Kuma a yanzu kaurin kwaltar titin ta nunka ta titunan da aka saba gani har sau biyu. Wani jami’in gwamnatin kasar ya bayyana cewa ginin hanya yana daya daga cikin manyan ayyukan da ake ci gaba da yi gabanin ranar bikin cika shekara 70 da kawo karshen yakin Duniya na Biyu. Kuma a lokacin bikin ne za a gudanar da wani babban faretin sojoji, wanda shi ne na farko a tarihin kasar da sojojin kasar za su yi tare da takwarorinsu daga wasu kasashen waje.

Abin Aajabi:- Sun manta da ’ya’yansu a kantin da suka yi sata


A makon jiya ne aka tsinci wasu yara a harabar wani babban kanti da ke Jihar Arizona ta kasar Amurka bayan iyayensu sun tsere, sun bar su a kantin da suka yi sata, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Metro ta bayyana ranar Litinin. ’Yan sanda sun bayyana cewa an tsinci yaron farko ne a wajen ajiye motocin kantin. Kuma suna zargin daya daga cikin barayin ce ta ajiye shi a wurin. Kodayake, daga bisani ’yan sandan sun gano wasu yaran a cikin wata mota wadanda ake kyautata zaton ’ya’yan barayin ne. Hakazalika, an yi nasarar damke iyayen yaran daga bisani. Iyayen biyu: Ashley Nicholas, mai shekara 20, da kuma Mattica Brock, mai shekara 30. Kuma ana zargin su ne da laifin sata da kuma jefa ’ya’yansu cikin hadari. Kodayake, jami’an tsaron sun ce daya daga cikin barayin ba ta kai ga shiga hannu ba tukuna.

Sojojin Kamaru sun yi zanga-zanga


Wasu sojojin Kamaru da suka yi aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen waje sun gudanar da zanga-zangar lumana a Yaounde domin matsa wa hukumomi su biya su hakkokinsu. Sojojin wadanda suka yi aiki a Jamhuriyar tsakiyar Afrika a lokacin da tashin hankali ya mamaye kasar, sun yi jerin gwano ne daga ofishin Firai minista zuwa ma'aikatar tsaro, suna neman kungiyar hadin kan Afrika watau AU ta biyasu hakkokinsu na tsawon shekaru biyun da suka yi aiki a kasar waje. Wasu majiyoyi sun ambato sojojin suna cewa duk da shigar da korafe-korafensu a gaban ma'aikatar tsaro, da kuma ganawar da suka yi da ministan tsaro har a yanzu ba su samu bayanai masu gamsarwa ba game da matsayinsu. A kan haka ne suka yanke shawarar yin zanga-zangar Hakan ya kai ga rufe wasu manyan tituna a birnin Yaounde da kuma takaita zirga-zirgar ababen hawa. Ana sa ran cewa kakakin gwamnatin Kamaru, Issa Tchiroma Bakary zai yi wa manema labarai bayanai kan wannan batun.

Microsoft na fafatawa da gwamnatin Amurka


Miscrosoft zai koma kotu domin ci gaba da rikicin da yake game da bukatar gwamnatin Amurka na cewa ya mika wasu sakonnin email da yake ajjiye da su a wata cibiyar tattara bayanai dake kasar Ireland A shekarar 2014, wata kotu ta yanke hukuncin da ya goyi bayan ikirarin da gwamnatin Amurka ta yi na cewa saboda tana da hurumi akan kamfanin dake da ofis a Amurkar, za ta iya tilasta masa mika mata bayanan da yake da iko da su ko da ace a wata kasar ake ajjiye da su Amma kamfanin Microsoft ya bada shawarar cewa hakan ya sabawa dokokin sirri A madadin haka kamfanin ya ce dole ne Amurkata mutunta 'yancin wasu kasashensannan kuma ya nuna alamun cewa Washington ta yi amfgani da yarjejeniyar taimakon Alkalai idan har tana son samun sukunin wadannan bayanai daga kasar Irelans da kuma wasu cibiyoyin tattara bayanai dake wajen Amurkar Tuni kasar Ireland ta ce ta na duba wannan bukata cikin gaggawa Wannan sain-sa zai nuna karfin da Amurka ke da shi a kan kamfanonin dake cikin kasar.

Masu amfani da WhatsApp 200m na cikin hadari


Kamfanin Checkpoint da ke son inganta tsaro a intanet ya ce kimanin mutane 200m da ke amfani da manhajar WhatsApp na fuskantar hadarin kutse daga 'yan damfara. A cewar kamfanin, masu kutse ka iya yin kutse cikin wayar mutum, kuma su hana shi amfani da bayanan ciki har sai ya biya su. An sanar da kamfanin WhatsAppa a kan wannan matsalar a karshen watan jiya, kuma ya dauki matakan gaggawa ta hanyar bai wa masu mu'amala da shi damar sabuntawa manhajar. Kamfanin Checkpoint ya yi kira ga masu amfani da WhatsApp da su sabunta manhajar domin cin gajiyar maganin da kamfanin ya samar na dakile barazanar masu kuste. An yi kiyasin cewa mutane sama da miliyan 200 ne ke amfani da manhajar WhatsApp ta hanyar intanet ko a komfuta, kimanin miliyan 900 kuma ke amfani da manhajar a wayoyin hannu. Kamfanin Facebook ya sayi WhatsApp a shekarar 2014 a kan $22m.