Translate site

Wednesday 2 September 2015

Siffofin “Windows 10” da alakarta da “Windows 7” da “Windows 8”

Ranar 29 ga watan Yuli ne kamfanin Microsoft ya kaddamar da sabuwar babbar manhajarsa mai suna “Windows 10.” Wannan ita ce sabuwar babbar manhajar da kamfanin ya sake ginawa tun bayan kaddamar da babbar manhajar “Windows 8” a shekarar 2012. Duniyar fasahar sadarwar zamani ta karkatar da hankalinta gaba daya zuwa kamfanin Microsoft a wannan rana, don ganin irin nau’in babbar manhajar da kamfanin zai fitar, wanda a baya yayi ta kuranta siffofinta, da yadda za ta sha bamban da wadannan Windows 8” da “Windows bista. ” Malam Bashir Sa’ad Abdullahi, babban editan Sashen Hausa na BBC da ke nan Abuja, Najeriya, ya yi hira da ni a ranar da aka kaddamar da wannan babbar manhaja, kuma sun sanya hirar a shirinsu na rana nan take. Sai dai ganin cewa hirar tana da tsawo, sun sanya wani bangare ne kawai, don karancin lokaci. Wannan ya sa na ga dacewar rubuce hirar gaba daya, don amfanin masu karatu. A sha karatu lafiya. BBC: Da farko, Baban Sadik za mu so ka yi mana bayani kan wannan sabuwar babbar manhaja da kamfanin Microsoft ke kaddamarwa a yau. Wane bayani za ka yi wa masu sauraronmu? Baban Sadik: Da farko dai, a halin yanzu da muke magana (29/07/2015 - 2.17pm), kamfanin Microsoft ya saki sabuwar babbar manhaja, wato: Operating System, mai suna “Windows 10” wadda aka jima ana ta jira. Kuma daman sun sanya lokaci cewa ranar 29 ga watan Yuli ne za a kaddamar da wannan babbar manhaja. Kuma da dama cikin jama’a sun kagara su ga irin abubuwan da wannan babbar manhaja ta kunsa. Duk da cewa akwai masana kwararru kan harkar sadarwa da kwamfuta (Debelopers) sama da miliyan daya da kamfanin ya basu damar yin gwaji (Test Running) a lokuta daban-daban. Sun gama gwajin, kuma a yau ake kaddamar da wannan babbar manhaja. Ni kaina yanzu haka da nake magana da kai, kwamfuta ta tana can tana saukar da wannan sabuwar babbar manhaja. BBC: Meye bambancin wannan babbar manhaja da kamfanin na Microsoft ke fitarwa a yau da kuma “Windows 7” ko “Windows 8,” tunda wannan “Windows 10” ce a turance; meye bambancinsu da manhajojin da kamfanin ya fitar a baya? Baban Sadik: Kafin muyi bayani a kan bambance-bambancen dake tsakaninsu, yana da kyau mu san babban dalilin da yasa ita kanta wannan babbar manhaja ta bayyana a wannan lokaci. Domin... BBC: To, me yasa wannan babbar manhaja take bayyana a wannan lokaci? Baban Sadik: Da farko dai kamfanin Microsoft ba shi da wata ka’ida na shekarun sake fitar da wata babbar manhaja. Idan muka duba lokacin da ya fitar da babbar manhajar “Windows dP” sai da tayi shekaru 16 ana amfani da ita. Sannan daga baya aka dakatar da ita aka kawo “Windows bista.” Manhajar “Windows bista” manhaja ce da sadda aka fitar da ita bai kamata a ce an kaddamar da ita ba. Domin ba a gama kayatar da ita ba. Don haka, ko da ta fito sai ya zama kamfanoni da dama da sauran jama’a masu amfani da “Windows dP” suka ki yin “Upgrading” (tsallakawa daga karamar babbar manhaja zuwa na sama da ita), saboda matsalolinta sun yi yawa. Wannan ya sa kamfanin ya canza akala ya fitar da “Windows 7,” cikin kasa da shekaru biyu. Wanda wannan (shi ne mafi takaituwar lokaci da kamfanin ya taba fitar da wata babbar manhaja). Bayan “Windows 7” ta bayyana, jama’a sun samu gamsuwa matuka da tsarinta sosai idan ka kwatanta ta da ainihin “Windows bista.” To ana cikin haka kuma, sai ya zamanto - tunda damas Microsoft kamfani ne na kasuwanci, lokuta daban- daban yana duba abin da ya dace da ka’idarsa ta kasuwanci ce ko fa’idar da yake son samu a kan kowace haja ya fitar - bayan bayyanar “Windows 7,” wanda galibin jama’a sun fi gamsuwa da ita fiye da “Windows bista,” kwatsam sai suka ce ga “Windows 8.” Da “Windows 8” ta bayyana sai aka ga kusan dabi’unta daya ne da na “Windows bista”; duk da cewa “Windows bista” ta fi ta muni (wajen mu’amala). Sai dai ita “Windows 8” tana da wahalar sha’ani ne. Wanda kuma kowa ya san kamfanin Microsoft ne a asali wajen iya gina manhajoji masu saukin mu’amala. (Wanda shi ne kamfanin da ya daukaka tsarin “Graphical User Interface,” wato tsarin dake sawwake wa mai kwamfuta mu’amala da ita ta hanyar kafofi masu sauki da gamsarwa) Kuma wannan ne ma ya bai wa kamfanin shahara a duniya. Kusan kashi 90 cikin 100 na masu amfani da kwamfutoci a duniya suna amfani ne da babbar manhajar Windows. Amma (abin mamaki) sai ya zama “Windows 8” ta zama mai wahalar mu’amala; ga kyale-kyale ga komai, amma ba kowa ke iya mu’amala da ita ba (sai kwararru na musamman). Wannan ya sa da dama daga cikin jama’a suka daina amfani da ita, wasu ma ba su sayi babbar manhajar ba. Sannadiyyar haka kamfanonin (kera kwamfuta) da dama irin su HP, da Toshiba, (da Dell, da Acer) suka yi asara. Ganin haka ne ya sa kamfanin Microsoft yin wani yunkuri wajen canza dabi’ar Windows, ta hanyar cakuda dabi’ar “Windows 7” da “Windows 8” a hade, wanda shi ne abin da ke cikin “Windows 10” da suke fitarwa a halin yanzu. Zan ci gaba mako mai zuwa in Allah Ya yarda.

Google da Apple sun kulla dangantaka

Kamfanin Google ya mayar da manhajarsa ta Android wadda za a iya daurawa ta yi aiki da ta Kamfanin Apple a manhajar iOS. Wannan ci gaba na nufin cewa masu agogon hannu na manhajar Android za su iya amfani da wayar salula ta iphone a karo na farko. Hakan dai zai habaka kasuwar agogunan hannu na zamani kuma zai zama kalubale ga kamfanin nan Apple. Wannan sabon ci gaba na nufin masu agogon hannun za su iya kiran waya ko su amsa kira. Haka kuma za su iya duba sakonnin ka-ta-kwana na text, har ma da duba lafiyar zuciyarsu ta hanyar yadda ta ke bugawa.

Mazauna Gamboru sun yaba wa sojin Nigeria

Wasu 'yan asalin garin Gamborun Ngala da ke jihar Borno Najeriya wadanda yanzu ke samun mafaka a wasu wurare sun ce suna murna sosai da nasarar da Allah ya ba wa sojojin Najeriya ta kwato garinsu. Sai dai sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba su izinin komawa gidajensu ba tare da bata lokaci ba, suna masu cewa ya kamata gwamnatin ta taimaka musu wajen gyara gidajen da aka lalata musu sakamakon hare-haren Boko Haram. A cewar su, suna cikin mawuyacin hali da suka hada da rashin kudi da rashin sanao'i da abinci. A ranar Talata ne rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kwato garin Gamborun Ngala wanda ke karkashin ikon mayakan kungiyar Boko Haram. Garin yana da matukar muhimmanci ta fuskar kasuwanci, domin kuwa yana hada kasashen Najeriya da Nijar da ma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Sojin Nigeria sun kwato Gamboru Ngala

Rundunar sojin Najeriya ta kwace ikon garin Gamboru Ngala, da ke jihar Borno daga hannun mayakan Boko Haram a ranar Talata. A wata sanarwa da rundunar ta fitar, mai magana da yawun rundunar Kanal Sani Usman Kuka-Sheka ya ce yanzu haka dakarun suna ta kokarin tattaro kayan aikinsu da kuma motocin sintiri. Dakarun sojin Najeriyar na cikin murnar wannan galaba da suka samu a kan Boko Haram. A baya sojojin Chadi sun karbo garin a hannun 'yan Boko Haram, amma daga bisani kuma suka sake karbe wa