Ana zargin mayakan Boko Haram na zuba guba a rijiyoyi da rafuka a wasu kauyukan da aka kore su a jihar Borno da ke arewacin Nigeria.
Rundunar sojin Nigeria a Maiduguri ta ce bayanan da ta samu sun nuna cewar 'yan Boko Haram na aikata wannan ta'asar a garuruwan da dakaru suka kore su.
Wata sanarwa da mai magana da yawun soji a Maiduguri, Kanar Tukur Gusau ya fitar, ta ce yanzu haka akwai shanun da suka mutu sakamakon shan ruwan wani rafi da aka saka guba.
Sanarwar ta bukaci al'ummar yankin su guji shan ruwan da ba a tantance inda aka debo shi ba, saboda gudun fadawa cikin hadari.
A cewar rundunar sojin akwai rafin da aka zuba guba a cikinsa a kauyen Kangallam da ke kan hanyar Marte zuwa Abadam.
Rundunar sojin ta ce za ta ci gaba da kokari domin kawar da 'yan Boko Haram daga maboyarsu
No comments:
Post a Comment