A makon jiya ne aka tsinci wasu yara a harabar wani babban kanti da ke Jihar Arizona ta kasar Amurka bayan iyayensu sun tsere, sun bar su a kantin da suka yi sata, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Metro ta bayyana ranar Litinin.
’Yan sanda sun bayyana cewa an tsinci yaron farko ne a wajen ajiye motocin kantin. Kuma suna zargin daya daga cikin barayin ce ta ajiye shi a wurin. Kodayake, daga bisani ’yan sandan sun gano wasu yaran a cikin wata mota wadanda ake kyautata zaton ’ya’yan barayin ne.
Hakazalika, an yi nasarar damke iyayen yaran daga bisani. Iyayen biyu: Ashley Nicholas, mai shekara 20, da kuma Mattica Brock, mai shekara 30. Kuma ana zargin su ne da laifin sata da kuma jefa ’ya’yansu cikin hadari. Kodayake, jami’an tsaron sun ce daya daga cikin barayin ba ta kai ga shiga hannu ba tukuna.
No comments:
Post a Comment