A shekaran jiya Laraba ne masu bincike a Jami’ar Birmingham da ke kasar Biritaniya suka ce sun gano takardun Al-kur’ani ( Bugun Hannu) da suka fi tsufa a duniya, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito.
Masu binciken sun ce wani nazarin kimiyya da suka yi a kan takardun sun nuna cewa an wallafa su ne fiye da shekaru 1,370 da suka wuce. Sun kuma ce takardun suna ajiye ne tare da wasu littattafan yankunan Gabas-ta-Tsakiya, inda bincike ya nuna cewa wani masanin tarihi dan asalin kasar Iraki, mai suna Alphonse Mingana, ne ya kai takardun jami’ar a shekarun 1920.
An ce mai yiwuwa mutumin da ya rubuta Al-kur’anin ya taba haduwa da Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ko kuwa ya taba jinsa lokacin da yake wa’azi.
Wani masani kan dakunan adana littattafai a Birtaniya, Dokta Muhammad Isa Waley ya ce, “wannan wani abu ne da Musulmi za su yi farin ciki da shi”
No comments:
Post a Comment