Jami'an gwamnatin Amurka sun ce wadan da su ka yi kutse a cikin shafukan intanet na gwamnatin sun sace bayanan zanen yatsun hannu wadanda yawansu ya zarce yadda ake zato.
A wata sanarwa da fadar gwamnatin ta white house ta fitar ta ce bayanan zanen yatsun hannu sama da miliyan 5 da 600,000 aka sace daga ofishin kula da ma'aikata.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa bayanan yatsun hannu miliyan 1 da 100,000 ne suka bace.
Ofishin ma aikatan OPM na matsayin wurin adana bayanan ma'aikata na gwamnatin Amurka ne a inda aka ajiye bayanai na ma'aikatan gwamnatin tarayya milyan 21 da 500,000.
An gano kutsen ne a watan Afrilun wannan shekara a inda aka ga masu kutsen su na satar shaida da kuma da izinin tsaro ma aikatan gwamnatin Amurkan.
Ciki har da lambar tsaro ta dan kasa da sunaye da adireshi da bayanan lafiya da na kudade da kuma bayanan tsaro na zanen hannu.
Hukumar tsaro ta FBI da ma aikatar tsaro ta Pentagon da kuma hukumar kula da tsaron cikin gida na cikin wani shirin gangami na jami'an tsaro na kar-ta-kwana na nazarin tasirin batar zanen hannu zai iya shafar wadan da aka yiwa satar.
A cewar Ken Munro jami'in wani kamfanin tsaro, "abu ne mai sauki a sake kalmar ko lambar sirri bayan an yi kutse, amma yana da matukar wahala a samu sabbin yatsu".
Sanarwar satar ta zo daidai da lokancin da shugaban China Xi Jingping ya ke ziyara a Amurka. Kwararru a harkar tsaro na zargin China da zama tushen kutsen da kuma satar bayanan, zargin da Chinan ta yi ta musantawa.
Ana sa rai Shugaba Obama da Xi jinglin za su tattauna matsalar tsaro a yanar gizo a ganawar da za su yi a makon nan.
No comments:
Post a Comment