Kamfanin jiragen sama na Indiya yana shirin rage
ma'aikatan jirgi su kimanin 125, saboda a cewarsa sun yi
kiba da yawa.
Wani jami'in jiragen sama na Indiya ya shaida wa BBC cewa an
dauki matakin ne saboda bin dokar da hukumar zirga-zirgar
jiragen sama ta bullo da ita wadda ta shafi nauyin jiki a bara.
Jami'in ya ce kamfanin jiragen saman ya gargadi ma'aikatansa
kimanin 600 su rage kiba, amma har yanzu 125 daga cikinsu ba
su rage kibar yadda ake bukata ba.
Ya ce an lura cewar ma'aikatan cikin jirgi masu kiba ba sa iya
taimakawa yadda ya kamata a lokacin da wani al'amari da ke
bukatar taimakon gaggawa ya faru.
No comments:
Post a Comment