Amma alhamdulillahi zamu ce wannan abu bai
shafe su ba ta bangare rasuwa ba sai dai an
samudan kalilan na mutum ukku zuwa hudu da
suka samu raunuka wadanda kuma raunukan ba
wadanda suke barazana bane ga ainihi rayuwar
su.
Mutanen da kace sun samu raunukan an basu
gado ne ko kuwa sun tafi sun ci gaba da harkokin
su?
‘’A’a kamar yadda nayi bayani ai ba wani abu
bane, irin dai dan buguwa ne haka, abubuwa ne
ba masu tada hankali ba, wasun ma an basu
magani an sallame su, akwai wadanda ma suka
dimauta suka gigita kwarai da gaske, kuma
hukumar Saudiyya duk ta kula da irin wadannan
Alhazzai kuma an basu tallafin da ya kamata
kuma an salami kowa ya tafi gida cikin namu
mutanen’’
Ambasada kunbi dukkan masaukin alhazzan
Najeriya kuka tabbatar kowanne na cikin koshin
lafiya ko ko ta wane hanya kuka gane cewa ba
wani dan Najeriya da wannan abu ya rutsa
dashi?
‘’Dama duk lokacin da alhaji yazo nan ko a
makka ko Madina ko ina ma yake , a ko wane
lokaci akwai ido akan sa tunda anan mutum ba a
gida yake ba, don haka wajibi a kowane lokaci
cikin awa 24 akwai jamiai da ke tare dashi akwai
na jihohi akwai na hukumar Alhazai, akwai
jamian ofishin jakadanci da ako wane lokaci suke
aiki suke sa ido akan halin da alhaji yake ciki’’
No comments:
Post a Comment