Shugaban hukumar tace fina finai ta jihar Kano da ke Najeriya, Sama'ila Na abba Afakallah, ya ce fina-finan Indiya da aka fassara su zuwa harshen Hausa ba bisa ka'ida, tamkar satar fasaha ce.
Afakallah ya shaida wa BBC cewa ya kamata masu fassara fina finan su bi doka da tsari na duniya, ciki har da samun izinin hakkin mallakar fina finan gabanin fassara su, yana mai cewa amma ba sa yi.
A cewar sa, daga yanzu, hukumarsa ba za ta sake amincewa da duk wani fim da aka fassara daga Indiya ko Amurka, da sauran harsuna ba, sai ta tabbatar cewa wadanda suka fassara su, sun bi ka'idoji.
Fina-finan Indiya da ake fassara su zuwa harshen Hausa suna kara farin jini a Najeria, suna kuma barazana ta fuskar kasuwanci ga fina finan Hausa, Kannywood.
No comments:
Post a Comment