Translate site

Thursday, 17 September 2015

An gano matsalar kulle waya a manhajar Android


Masu bincike a jami'ar Texas sun gano wata matsala a manhajar Android da ka iya ba mutane damar bude wayar da aka kulle. Masu binciken su gano cewa ta hanyar amfani da kalmar sirri mai matsawo a matsayin mabudin wayar hannu ko tablet ka iya sa tsarin da ta ke aiki da shi ya wargaje a cikin wasu yanayi. A wannan matsalar ta fi faruwa ne a nau'in lollipop na manhajar Android na baya-bayan nan wanda ke amfani da shi a wayar hannu. Kamfanin Google ya foto da maganin wannan matsala ga samfurin Nexus a ranar Laraba. Kusan kashi 21 na wayoyi masu amfani da manhajar Android na aiki ne da wadanda suke da matsalar. Bayan ruguje tsaron, masu binciken sun samu damar bude bayanan da ke cikin wayar da kuma sauran abubuwan da ke ciki. Sai dai a cewar masu binciken za'a iya maganin matsalar idan mai na'urar ya yi amfani da zane ko lambar sirri a maimakon kalmar sirri a yayin kullewa.

No comments:

Post a Comment