Kamfanin Apple ya yi jinkiri wajen sabunta tsarin da agogon sa kirar WatchOS 2 ke aiki dashi, bayan ya gano wasu kura-kurai a cikin manhajar Agogon.
Apple ya yi niyyar sabunta manhajar Agogon na sa ne tare da wayar sa ta komai da ruwanka kirar iOS 9 .
A cewar wani kamfanin bincike mai suna IDC, Agogon kamfanin Apple ya kasance wanda yafi kasuwa da ake rububinsa a yanzu.
Sai dai kuma manhajar da ke cikin Agogon kamfanin a yanzu ba ta bayar da dama ga wata manhaja ta daban tayi aiki a cikin agogon ba.
Wani wakilin kamfanin ya shaidawa manema labarai cewa sun gano wasu kura-kurai a Agogon na su na Watch0S 2, a saboda haka za su dauki dan lokaci kafin gyara kura-kuran.
Wakilin kamfanin ya cigaba da cewa ba zasu samu damar fito da sabon agogon na su kirar WatchOS 2 ba a yan kwanakin nan, amma nan bada jimawa ba za a fito dashi.
A watan satumbar bara, kamfanin Apple ya nemi gafara masu hulda dashi bayan sabunta wayar su ta salula kirar iOS ya haifar da matsala ga wasu wayoyin su a inda ba a iya kiran waya da su.
A ranar laraba, kamfanin Google ya hanzarta magance matsalar wayar sa kirar Android OS bayan ya gano cewa za a iya bude wayar ta hanyar rubuta dogayen kalmomin sirri.
No comments:
Post a Comment