Wani gungun mahara masu kwace ta intanet ya sa Bankuna
da kafofin yada labarai da kamfanonin kera manhajar
wasanni a gaba.
Gungun ya sa su a gaba ne ta hanyar yi musu barazar su biya
su wasu kudadade ko su lalata shafukan na kasuwancinsu na
intanet.
A cikin wani rahoto da Akamai wani kamfanin intanet ya fitar,
ya ce a watanni 10 da suka wuce gungun ya kai wa masu ciniki
da su hari har sau 141 a intanet
Gungun maharar ta intanet da ake kira DD4BC ya yi barazanar
makare rumbun ajiyar bayanan kamfanin idan bai biya fansar
kudin intanet bitcoin 50 kimanin £8,000 ba.
Gungun na kai hari a shafukan intanet ta hanyar cika shafin
wanda ya ke hari da ambaliyar gigabits 56 na bayanai a dakika
1.
A cewar rahoton Akamai gungun maharan na DD4BC na nan
tun cikin watan Satumba na 2014 sai dai a kwanakin nan ne ya
matsa kaimi da kai hari akan harkokin kasuwanci a intanet.
Harkokin hada-hadar kudi na daya daga cikin inda gungun ya
matsawa lamba ta hanyar kwace da cin zarafi da batanci da
kuma sa a ji kunya a idon jama'a a cewar Stuart Scholly
shugaban tsaro na kamfanin Akamai.
No comments:
Post a Comment