Jam'iyar PDP da ta sha kaye a jihar Bauchi ta
dauki matakin gyara kura kurai da tace an
tafka da ya janyo mata faduwa zabe bara,. Ta
kuma sauke wadansu shugabannin jam'iyar
tare da barazanar kaisu gaban hukumar EFCC
Jam’iyar adawa ta PDP a jihar Bauchin Najeriya
ta gudanar da garambawul da ya kai ga tsige
shugaban jam’iyar da sakataren jihar, da kuma
zaben shugabannin wucin gadi tare da
barazanar yiwuwar sa bakin hukumar yaki da
cin hanci da rashawa ta kasar EFCC.
Mataimakin shugaban jam’iyar kuma dan
kwamitin zartaswa Salihu Ya’u Nabardo ya
yiwa wakilinmu Abdulwahab Mohammed karin
haske dangane da batun.
No comments:
Post a Comment