Shafin sada zumunta na Facebook zai kaddamar da wani tauraron dan-Adam wanda zai rika samar da intanet a yankunan karkara na Afirka.
Mutumin da ya mallaki shafin, Mark Zuckerberg, ya ce za su hada gwiwa da kamfanin tauraron dan-Adam da ke Faransa, Eutelsat, domin kaddamar da shi a watanni shidan farko na shekarar 2016.
Mark Zuckerberg ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "Za mu ci gaba da aiki domin ganin mun samar da intanet a dukkan sassan duniya komai nisan wurin kuwa."
Wannan mataki yana cikin shirin Facebook na samar da shafin intanet mai suna Internet.org, wanda ya yi ta shan suka a kasashe da dama.
A wasu yankunan kasar Indiya, mutane sun fusata da matakin na Facebook, suna masu cewa hakan zai fifita shi a kan wadanda ke gogayya da shi.
Internet.org yana duba hanyoyi daban-daban da zai iya samar da intanet a wurare masu sarkakiya.
A kwanakin baya, kamfanin ya ce zai yi amfani da jirage marasa matuka domin samar da intanet a yankuna masu wahalar zuwa.
No comments:
Post a Comment