A karon farko kamfanin Daimler na Jamus ya yi gwajin wata babbar motar daukar kaya maras direba.
Daga an taba wani dan maballi a motar sai ta soma sarrafa kanta da taimakon 'highway Pilot' na'urar da ke taimaka mata kaucewa sauran masu amfani da hanyar.
Sai dai kamfanin ya jaddada cewa sharadi ne wani ya kasance a cikin motar ya kuma sa ido a kan hanya a kowanne lokaci.
A farkon shekarar nan ne kamfanin Daimler ya nuna aniyarsa ta yin wannan gwaji a karshen shekara ta 2015.
Na'urar na iya gane alamun kan hanya da sauran motoci da kuma duk wani abin da zai sha gabanta, ta hanyar amfani da kyamara da kuma wata na'ura mai iya gane abubuwa wacce aka makala a gaban motar daukar kayan.
A wani taron 'yan jaridu Mista Bernhard ya jaddada ingancin na'urar dari bisa dari wajen kare haddura saboda, a cewarsa, ba ta gajiya, ba ta shiga sabga kuma tana nan a ko da yaushe.
Motar ba ta da matsala
"Da zaran mun hau babbar hanya za mu sa motar ta soma tuka kanta" in ji Wolfgang Bernhard shugaban kamfanin Daimler a yayin da ya soma tuka babbar motar daukar kaya kirar Mercedes-Benz Actros kan wata babbar hanya mai cike da motoci a garin Baden-Wurttengerg a makon da ya wuce.
Yana latsa wani shudin maballi a gaban motar sai ta fara sarrafa kanta.
A cikin nasara babbar motar ta tuka kanta a kan babbar hanyar garin har sai da ta kai gudun kilomita 80 a sa'a guda.
Mista Bernhard da Mista Winfred Kretschemann, Minista kuma shugaban garin Wurttenberg suna gaban motar tana tafiya suna kuma shan gahawa.
Mista Bernhard ya ci gaba da yi wa abokin tafiyar ta sa bayanin fasahar da motar ta ke da ita.
No comments:
Post a Comment