Yara suna karatu a karkashin bishiya a sansanin
yan gudun hijira a garinMaiduguri
See comments
Share
A taron manema labarai babban magatakardan
hukumar a Najeriya Farfesa Abdulrasheed Garba
yace sakamakon ya nuna sama da kashi 68 na
wadanda suka rubuta jarabawan sun samu
nasarar da ake bukata a darasin turanci da lissafi.
Wanda wannan ya nuna cewa jarabawar ta bana
an samu ci gaba.
Farfesa Abdulraseed Garba yace akwai dabarun
da hukumar
tayi a lokacin jarabawar.
‘’Abinda muka yi shine muka tabbatar cewa duk
tambayar da za ayi to ta fito daga cikin
abubuwan da aka amince a koyar a makarantun
sakandare, wannan yasa muka samar da
dangantaka tsakanin hukumar ta NECO da
hukumar NRDC, Wannan hukumar ta NDRC ita ce
keda allhakin fitar da jadawalin koyarwa’’
A wannan shekarar kuma satar jarabawar bai kai
na shekar bara ba.
‘’Labari mai dadi shine magudin da aka samu a
wannan shekar bai kai na bara ba domin duk
dabarar da kayi sai ka samu magudi amma
wanna shekarar bai kai na bara ba, duk da haka
mun kakkama an tantance kuma an zakulo
wadanda suke da laifi da yawa an soke
sakamakon su.’’
Sai dai ya zuwa wannan lokaci hukumar ta NECO
tace tana bin wasu jihohi bashin kudin jarabawan
su da basu biya ba, kamar yadda Farfesa
Abdulrasheed yayi Karin bayani.
No comments:
Post a Comment