Matuka manyan motocin dakon kaya suka cika kan
manyan hanyoyin faransa domin nuna rashin
amincewarsu da shirin garambawul din fansho.
See comments
Share
Masu manyan motoci wanda ke dakon kaya sun
fara yajin aiki a birnin lagos domin adawa da
dokara hana zirga zirga a titunan birnin daga
karfe 6 na safiya zuwa 9 na dare.
Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin
jihar Lagos ta yiwa masu motocin dakon kaya a
birnin cewa su kiyaye hanyoyin birnin karfe 6 na
safiya zuwa karfe 9 na dare. Uwar kungiyar masu
motocin dakon kayan sun fara wani yajin aiki
yajin aikin da sai baba ta gani, domin tilastawa
gwamnatin jihar janye wannan umarni nata.
Yanzu haka dai harkokin yau da kullum na
neman tsayawa cik a babbar tashar jiragen ruwa
na kasar inda akasarin masu dakon kayan ke
dauko kayansu zuwa wasu sassa daban daban na
Najeriya. wannan lamari ya shafi masu hada
hadar harkar gwari a birnin na Lagos, al’amarin
da ka iya tada farashin kayayyakin saye da
sayarwa dama na kasuwanni daban daban dake
jihar dama wasu sassa na tarayyar Najeriya.
Mataimakin shugaban masu dakon kaya a jihar
lagos Alhaji Abdullahi Jiji, yace “aikin mu ma da
rana ya aka kare ballan tana ace daga karfe tara
na dare zuwa karfe shida na safe, sau dayawa
ana kwace musu motoci da kaya ballantana da
daddare. Kuma ba zamu iya aiki a wannan
lokacin ba.”
Suma masu amfana da dagon da motocin keyi sun
yi kira ga gwamnatin jihar Lagos ne da ta duba
wannan doka da nufin sassauta shi
Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibril, ya
halarci taron satantawa da yan kungiyar da kuma
kwamishinan yansanda inda aka tashi taron ba
tare da matsayi ba.
No comments:
Post a Comment