Mai wa'azin addinin musulunci Shaik Usman
Bauchi yace a kwanaki dari na farkon mulkin
Buhari an samu takawa kungiyar Boko Haram
birki
Shaikh Dahiru Usman Bauchi yace an kuma samu
inganta rayuwar 'yan kasa tare da yaki da cin
hanci da rashawa.
Cikin kwanaki dari Allah ya nunawa al'ummar
Najeriya alamun cin nasara na zaman lafiya.
Kafin wannan lokacin yawancin yankunan
jihohin Yobe, Borno da Adamawa suna hannun
'yan Boko Haram ne amma yanzu an kwatosu.
'Yan Boko Haram sun yadu sosai saboda a rana
daya sun kashe mutane fiye da dubu biyu a Baga
suka cigaba da sarafa bom kusa da Ashaka kana
suna kai hare hare Nafada da Bajoga da Gombe
da Azare. Har cikin Masallacin Jumma'a na Kano
sun kai hari. Amma cikin kwanaki dari da Buhari
ya kama mulki Allah ya kawar dasu an zauna
lafiya.
Yanzu 'yan Boko Haram basu da karfin kai hari
saidai su ne ake kaiwa hari yanzu. Saboda
nasarar da Allah ya bayar suke gode mashi. Allah
kuma ya bada lafiya da zaman lafiya d kwanciyar
hankali.
Shaik Dahiru Bauchi bayan ya yi addu'a sai yace
dalilin tara taron malamai ke nan domin a yiwa
Allah godiya ta musamman.Ya godewa malaman
da suka kasance a wurin addu'an tare da
malaman da suka zauna garuruwansu ko
kauyukansu amma suka yi addu'a.
Da ya amsa tambaya akan salon mulkin Buhari
Shaik Bauchi yace shugaban na yaki da cin hanci
da rashawa kuma ana yi masa addu'a Allah ya
bashi nasara ya kuma ba kasar zaman lafiya ta
kowace hanya. Ya ce Allah ya sa a maido da
kudaden da aka kwashe domin an wawuresu an
kaisu wasu wurare kafin ya kama mulki.
No comments:
Post a Comment